26 Afirilu 2022 - 19:09
Ministan Tsaron Kasar China Zai Kawo Ziyara Iran

Kamfanin dillancin Labarun Iran na “ Irna” ya bayar da labarin cewa; Ministan tsaron kasar ta China Janar Wie Fenghe zai kawo ziyara Iran tare da babbar tawaga ta jami’an tsaron kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A gobe Laraba ne dai ministan tsaro kasar ta China zai zo Iran, inda zai gana da takwaransa na Iran Birgadiya Janar Ashtibani domin tattauna alaka a tsakaninsu.

Bugu da kari ministan tsaron na kasar China Janar Wie Fenghe zai gana da wasu manyan jami’an kasar ta Iran domin tattauna halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya da kuma duniya.

342/